Winamp Logo
Mu Zagaya Duniya Cover
Mu Zagaya Duniya Profile

Mu Zagaya Duniya

Hausa, Political, 1 season, 44 episodes, 14 hours, 36 minutes
About
Wannan Sabon Shiri ne da ke tattauna Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya. Ana gabatar da shirin ne a karshen mako.
Episode Artwork

Matakin hadin gwiwar da Nijar ,Mali da Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga ECOWAS

Daga cikin muhimman labarun makon jiya da shirin ya sake waiwaya domin bitarsu akwai, matakin hadin gwiwar da Nijar da Mali da kuma Burkina Faso suka dauka, na sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS.Sai kuma sake karya darajar Naira da gwamnatin Najeriya ta yi, karo na biyu  cikin watanni 8.A Turai kuwa, za a ji yadda zanga-zangar  manoma ta bazu zuwa sassan nahiyar saboda adawa da wasu sauye-sauyen mahukuntan kasashen yankin da suka ce ba za su lamunta ba.
2/3/202419 minutes, 58 seconds
Episode Artwork

Taron Shugabannin arewacin Najeriya don lalubo hanyar magance matsalar tsaron

Masu sauraro Assalamu alaikum, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI ke muku maraba cikin shirin Mu Zagaya Duniya da ke waiwaye gami da zabar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.
1/27/202419 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Rikici tsakanin 'yan ta'adda a arewacin Najeriya ya illata bangaren Dogo Gide

Shirin wannan makon zai fara ne da waiwayar bata-kashin da aka yi tsakanin ‘yan bindiga a Najeriya, lamarin da ya kai ga illata bangaren daya daga cikin jagoran ‘yan ta’adddan da ya addabi jama’a.Fira Ministan Jamhuriyar Nijar ya yi tatttaki zuwa Iran, bayan ganawarsa da mahukuntan kasar Rasha inda suka karfafa yarjejeniyar tsaron da suka kullla. A gabashin Afirka kuwa cibi ne ya zama kari, domin kuwa gwamnatin sojin Sudan ce ta katse alaka da kungiyar kasashen yankin gabashin nahiyar ta Afirka, saboda gayyatar shugaba kuma Janar Abdel Fattah al-Burhan da suka yi.
1/20/202420 minutes, 1 second
Episode Artwork

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Abba Gida-Gida a zaben gwamnan Kano

Cikin shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleiman, ya fara ne daga Kano a Najeriya, inda a ranar Juma’ar da ta gabata, kotun koli ta tabbatar da gwamna Abba Kabir Yusuf Abba na jam’iyyar NNPP a matsayin halastaccen gwamnan jihar. Shirin ya kuma sake waiwayar matakin jagoran mulkin Sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan na gindaya sharudda gabanin amincewa da shiga tattaunawa da bangaren jagoran dakarun RSF Mohamed Hamdan Dagalo da suka shafe fiye da watanni 9 suna gwabza yaki.
1/15/202420 minutes, 1 second
Episode Artwork

Gwamnatin Najeriya ta haramta karbar shaidar karatun digiri daga Benin da Togo

Daga cikin labarun da shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya sake waiwaya a wannan makon akwai matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na haramta karbar takardun shaidar kammala karatun digiri daga jami'o'in Jamhuriyar Benin da kuma kasar Togo. Shirin ya kuma leka yankin Gabas ta Tsakiya, inda aka kashe kusan mutane 100 a wani harin ta'addanci da aka kai a kasar Iran.
1/15/202419 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

Bitar wasu muhimman labaran da suka faru a duniya cikin wannan mako

Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai batun yadda yan ta'adda a Najeriya ke gina ramu  suna boyewa, saboda barin wutar da suke sha daga sojojin kasar, sai kuma batun kammala ficewar sojojin Faransa a Nijer da dai sauran manyan labaran da suka hada da  Burkina Faso, jamhuriyar Benin, yakin Isra'ila da Hamas, tare da dokar yan ci rani da Faransa ta amince da ita.
12/23/202320 minutes, 4 seconds
Episode Artwork

ECOWAS/CEDEAO ta tabbatar da juyin mulki aka yi a Nijar

Daga cikin labarun da Shirin ya kunsa akwai matakin da kungiyar kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ko CEDAEO ta dauka na amincewa da da cewar an yi juyin Mulki a Nijar, sannan kuma ta dakatar da ita daga cikin ta har sai lokacin da sojoji suka maida wa farar hula Mulki.A Najeriya kuma, Bankin Duniya ne ya bukaci gwamnatin kasar ta fadada tsauraran matakan da take dauka na yi wa tattalin arzikin kasar garambawul, domin ceto shi daga durkushewa baki daya a nan gaba.
12/16/202320 minutes, 31 seconds
Episode Artwork

COP28 - An samar da asusun tallafa wa kasashe don yaki da matsalar sauyin yanayi

Shirin "Mu zagaya duniya" na wannan makon tare da Khamis Saleh ya waiwari babban taron sauyin yanayi na COP28 da aka faro a Dubai, inda aka samar da wani asusu na musamman da manyan kasashe za su rinka zuba kudi don taimaka kananan kasashen da matsalar da ba su suka samar ba ta fi shafa. Haka nan shirin ya kuma duba matakin da gwamnatin sojin Nijar ta dauka na dakatar da dokar hana safaran bakin haure, matakin da EU ke ganin a matsayin wata barazana ta kara yawan bakin hauren da zasu kwarara kasashenta.Ku latsa a lamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......
12/2/202319 minutes, 46 seconds
Episode Artwork

Bitar wasu daga cikin labaran da suka dauki hankali na mako

Shirin zai kuma waiwayi kalaman da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayi kan cewa Dimokaradiyar kasashen yammacin turai fa ba ta haifa wa nahiyar Afirka da mai idanu ba.  Cikin makon da ya gabata, aka shiga rudani, yayin da kuma a gefe guda aka yi ta tafka muhawara a Kano dake arewacin Najeriya, bayan da kotun daukaka kara ta fitar da takardar hukuncin da ta yanke kan shari’ar zaben gwamnan jihar a juma’ar waccan makon da ya gabata, inda ta tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe.  Sai ku biyo mu..............
11/25/202319 minutes, 50 seconds
Episode Artwork

MU zagaya Duniya: Kotun daukaka kara a Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Kano

Ciki Shirin wannan makon za a ji cewar Kotun Daukaka karar Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben Kano da ya karbe kujerar Gwamnan jihar daga hannunn Abba Kabir Yusuf na NNPP ya mika ta zuwa Nasir Yusuf Gawuna na APC.Kasar Ghana ta bukaci hadin gwiwar kasashen Afirka domin tilasta wa kasashen da suka yi wa nahiyar mulkin mallaka biyansu diyya akan yadda suka azabtar da su da cinikin bayi. A Gabas ta tsakiya kuwa Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne ya zargi mayakan Hamas da dakile duk wani yunkuri na takaita yawan rayukan fararen hular da suke salwanta a Zirin Gaza.
11/18/202319 minutes, 55 seconds
Episode Artwork

wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a wannan makon

Halin da asibitoci ke ciki a Zirin Gaza, bayan da aka shafe sama da wata guda Isra’ila na ci gaba da ruwan bama-bamai kan Falasdinawa, wadanda ya zuwa yanzu akalla dubu 40 suka jikkata baya ga sama da 10 da suka mutu a Gaza tareda Nura Ado Suleiman.
11/11/202319 minutes, 58 seconds
Episode Artwork

Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da dubu 9,000, fiye da rabinsu kuma mata ne da kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya, ta bukaci a gaggauta tsagaita wuta a Zirin Gaza, tare da gargadin cewa lokaci na kurewa kasashe kan bukatar dakile yi wa Falasdinawa kisan kare dangi a yankin na Gaza. Shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Filpipo Grandi ya bukaci mambobin Kwamitin Tsaro na Majalisar da su kawo karshen rarrabuwar kawunan da ke tsakaninsu, don tabbatar da an tsagaita wutar da za ta dakatar da salwantar rayukan Falasdinawa a Zirin Gaza.
11/4/202320 minutes, 5 seconds
Episode Artwork

Muhimman labarun lamurran da suka wakana a cikin mako

Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta sun kai farmakin wucin gadi a arewacin yankin Zirin Gaza ta kasa a cikin daren ranar Alhamis, inda suka yi  arrangama da  mayakan Hamas a matsayin sharar fagen shirinta na kaddamar da gagarumin farmakin murkushe kungiyar ta Hamas
10/28/202320 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Harin asibitin Gaza ya jaanyo cece-ku-ce

 Cikin labarun da shirin makon nan ya waiwaya akwai Harin da ya kashe daruruwan mutane a babban asibitin Zirin Gaza, lamarin da fusata kasashe da dama, da hukumomi, da kungiyoyin na kasa da kasa, da sauran al’umma a sassan duniya. Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da dakile wani yunkurin hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum na tserewa daga gidan da ake tsare da shi. 
10/21/202318 minutes, 26 seconds
Episode Artwork

Halin da ake ciki a Zirin Gaza bayan barkewar yaki tsakanin Isra'ila da Hamas

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' da ya saba waiwayar labarun makon da ya kare a wannan karon ya mayar da hankali kan yakin da ya barke tsakanin Isra'ila da mayakan Falasdinawa na kungiyar Hamas. Za kuma a ji yadda dubban jama’a suka gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a sassan duniya, yayin da Amurka ta jaddada goyon bayanta ga Isra’ila.
10/14/202319 minutes, 59 seconds
Episode Artwork

Mu zagaya Duniya

Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin Shirin Mu Zagaya duniya daga nan sashin Hausa na Radio France International RFI………Nura Ado Suleiman zan jagoranci bitar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata.
10/7/202318 minutes, 56 seconds
Episode Artwork

Shirin Mu Zagaya Duniya

Masu sauraro Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin Shirin Mu Zagaya duniya daga nan sashin Hausa na Radio France International RFI………Nura Ado Suleiman zan jagoranci bitar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata. 
9/30/202319 minutes, 51 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da tarin daliban jami'ar Gusau

Shirin Mu zagaya duniya tare da Nura Ado Suleiman kamar kowanne mako ya yi bita ne kan muhimman labaran da suka faru a makon da muka yi bankwana da shi, inda a cikinsa za ku ji yadda 'yan bindiga suka sace gomman dalibai a Jami'ar tarayya ta birnin Gusau a jihar Zamfara. Haka zalika a cikin shirinza ku ji yadda Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sha alwashin daukaka kara bayan matakin kotun sauraren kararrakin zabe na kwace nasarar da ya yi a zaben watan Maris.Bugu da kari shirin ya leka sauran sassan Duniya dauke da muhimman labarai na wannan mako, ciki kuwa har da dambarwar bakin haure a Italiya baya ga ziyarar Sarki Charles na 3 a Faransa baya ga ziyarar Fafaroma Francis.Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
9/23/202320 minutes, 7 seconds
Episode Artwork

Mu Zagaya Duniya

Shirin Mu Zagaya Duniya na duba Wasu Muhimman Labarai da suka ja hankalin Duniya a cikin mako. Ana gabatar da shirin ne a ranar Asabar da safe a kuma maimaita ranar Lahadi da daddare.
9/16/202320 minutes, 2 seconds
Episode Artwork

'Yan adawa sun yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana bitar wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata. daga cikin abbubuwan da shirin ya kawo muku, za ku ji cewa, manyan jam’iyyun adawa a Najeriya sun yi  watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin saben shugaban kasa da ta tabbatar da nasarar da shugaba Bola Tinubu da ya lashe zaben da ya gudana a karshen watan Fabarairu. da sauransu.
9/9/202319 minutes, 1 second
Episode Artwork

Bitar labaran Mako; Yunkurin ECOWAS na daukar matakan soji a Nijar

Cikin batutuwan da Shirin wannan mako ya waiwaya tare da "Nura Ado Sulaiman", akwai matakin da kungiyar Kungiyar ECOWAS ta dauka na amince wa da shirin kafa rundunar soji ta wucin gadi wadda za a yi amfani da ita wajen kai hari a kan sojojin da suka yi juyin Mulki a Nijar, idan matakan diflomasiya suka gaza haifar da ‘da mai ido. Sakamakon takunkumai da suka hada rufe iyakoki, da kuma hana hada-hadar kudade da kasashen Yammacin Afirka suka kakaba wa Jamhuriyar Nijar, yanzu haka an fara fuskantar karancin naman kaji, kifi da ake shigar da su kasar.A cikin shirin, akwai batun, mutanen da suka rasa ‘yan uwansu ko kuma suka samu raunuka a sanadiyyar harin ta’addancin da aka kai wa ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Nairobin kasar Kenya a shekarar 1998, da suka bukaci Amurka ta biya su diyya, shekaru 25 bayan faruwar wannan lamari.
8/12/202320 minutes, 15 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran Mako; Katsalandan na kasashen ketare kan Nijar zai kara dagula lamura - Rasha

Tawagar kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta bar Jamhuriyar Nijar a yau Juma’a, ba tare da samun ganawa da Janar Abdurahman Tchiani, shugaban mulkin sojan da suka yi juyin mulki ba, yayin da a gefe guda Rasha ta ce shiga tsakani na kasashen waje ba zai warware lamarin kasar ta Nijar ba.  Ga alama mutane da dama na bayyana rashin amincewa da matakin na soji, kuma ko su shugabannin sojin da tsohon shugaban kasa Mahaman Ousmane da wasu ‘yan Najeriay da dama, na nunarashin amincewa da haka.Amma minister harkokin wajen Senegal ta bayyana cewar muddin ECOWAS ta bada umurni, toh zasu bada sojojin su domin daukar matakin soji akan Nijar. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
8/5/202319 minutes, 26 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako; Shekarar 2023 kan iya zama shekara mafi tsananin zafi a tarihi

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kasashen yankin arewacin duniya za su ci gaba da ganin tsananin zafi sakamakon dumamar yanayi da ke ci gaba da ta’azzara, gargadin da ke zuwa a dai dai lokacin da tuni nahiyar Turai da arewacin Amurka da kuma wasu sassa a Asiya suka fara ji a jikinsu.A cikin shirin mu zagaya Duniya Rukkaya Abba Kabara ta dubi a kan wannan labari da wasu a kai.
7/22/202319 minutes, 41 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran Mako ; Sai bayan Ukraine ta fita daga yaki za ta iya shiga NATO

Biden ya shaidawa taron manema labarai a kasar Finland kwana guda bayan taron kungiyar inda mambobin kungiyar suka gaza baiwa Ukraine damar shiga NATO, "Ba batun shiga ko akasin haka bane, lokaci ake jira. Biden ya gana da shugabannin yankin Nordic a Helsinki na kasar Finland,Shugaba Niinisto ya karbi bakuncin taron da ya samu halartar firaministan Sweden, Norway, Denmark da kuma Iceland.A cikin shirin mu zagaya Duniya Rukkaya Abba Kabara ta dubi a kan wannan labari da wasu a kai.
7/15/202319 minutes, 33 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Bankin duniya ya tallafawa kasashen Tafkin Chadi da dala dubu 1

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda bankin diniya ya tallafawa kasashen da ke yankin Tafkin Chadi da dala dubu daya, don murmurewa daga komabayan da suka samu sabida rikicin Boko Haram. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
7/8/202319 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen zaman sojojin a Mali

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen zaman sojojinta na MUNISMA a Mali, bayan da suka kwashe tsawon shekaru 10 suna aiki. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman.....
7/1/202319 minutes, 58 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Wasu attajirai 'yan yawon bude ido sun mutu a tekun Atlantic

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa, ciki har da yadda shugabanin wasu kasashen Afirka suka caccaki manyan kasashen duniya kan yadda suke zuba makudaden kudade a Ukraine, ba tare da duba halin da Afirka ke ciki ba, sai kuma labarin mutuwar wasu hamshakan attajirai masu yawon bude ido a kokarinsu na ziyarar sauran tarkacen jirgin ruwan Titinic.
6/24/202320 minutes, 25 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Hadarin kwalekwale ya hallaka mutane sama da 100 a Najeriya

Shirin 'Mu zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitar wasu labarai da suka fi daukar hankali cikin mako mai karewa ciki harda hatsarin kwale-kwale da yayi sanadiyar mutuwar sama da mutane 100 a jihar Kwara dake Yammacin Najeriya.
6/17/202319 minutes, 54 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako - Harin Al-shebaab sansanin dakarun AU a kasar Somalia

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu labaran da suka fi daukar hankali cikin makon da muka yi bankwana da shi, masamman harin da mayakan Al-shebaab suka yi sansanin dakarun AU dake Somalia. Sai kuma korar da shugaban Rwanda Paul Kagame ya yi wa wasu manyan hafsoshinsa.
6/10/202321 minutes, 7 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Janye tallafin mai a Najeriya

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ta wannan mako tare da Nura Ado Suleiman ya yi bitan wasu labaran da suka wakana a makon da muka yi bankwana da shi masamman batun janye tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tunubu ya sanar.
6/3/202320 minutes, 14 seconds
Episode Artwork

Bitar labaran mako: Kungiyar kasashen Afirka ta ci ka shekaru 60 da kafuwa

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' da ke waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a  cikin maako mai wucewa tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya waiwayi bukin ciki shekaru 60 da kafuwar kungiyar kasashen Afirka, a Najeriya 'yan kasar sun bayyana abin da suke so sabuwar gwamnati mai kamawa ta yi musu.
5/27/202320 minutes, 22 seconds
Episode Artwork

Mutane 10 sun mutu a wani sabon rikici da ya barke a jihar Filato da ke Najeriya

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako kamar yadda aka saba, ya waiwayi muhimman  abubuwan da suka faru a duniya a makon da ya gabata. Daga cikin akwai halin da ake ciki a jihar Filato, inda aka akalla mutane 100 suka rasa rayukansu sakamkon wani sabon rikici da ya barke, da kuma shugabannin kasashen Afirka shida da za su yi tattaki zuwa Rasha da Ukraine, domin sulhunta yakin da kasashen suka shafe sama da shekara 1 suna gwabzawa.  
5/20/202320 minutes, 16 seconds
Episode Artwork

Rahoton MDD ya bankado kisan fararen hula da sojoji suka yi a Mali.

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya saba waiwayar mahimman abubuwan da suka faru a duniya a  cikin maako mai wucewa. Daga cikin abubuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon, akwai rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ya bayyana cewar sojojin Mali tare da dakarun kasashen ketare da ke taimaka musu a yakin da suke yi da taa'addanci sun kashe daruruwan fararen hula a shekarar 2022. Zaloka, baangarorin da ke riki da juna a Sudan sun bada dama a shigo da kayayyakin agaji inda ake da bukata.
5/13/202321 minutes, 3 seconds
Episode Artwork

Yadda bikin ranar ma'aikata ta duniya ya gudana

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako kamar yadda aka saba a kowane mako ya duba manyan abubuwan da suka wakana ne a makon da ya gabata. Shirn ya duba yadda aka gudanar da bikin ranar ma'aikata ta duniya a wasu sassan duniya, sannan ya duba batun rikicin da ya baarke a ksar Sudan, da irin kokarin da kasashen duniya ke yi na warware shi tun bayan da ya tashi a ranar 15 ga watan Afrilu a tsakanin rundunar sojin kasar da dakarun kai daaukin gaggawa na musamman.
5/6/202322 minutes
Episode Artwork

Jiragen yakin sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai kan dakarun RSF a Khartoum

Jiragen yakin sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai kan dakarun RSF a Khartoum, duk da kara wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi da kwanaki 3.Gwamnatin Najeriya, ta soke shirin janye tallafin man fetur kafin mika ragamar mulki ga hannun sabuwar gwamnati.. Nura Ado Suleiman  a sabon shirin da ya saba waiwayar wasu daga cikin muhimman al’amuran da suka auku a makon da ya gabata, a cikin shirin ‘Mu Zagaya Duniya’ wanda ke zuwa daga sashin Hausa na RFI.
4/29/202318 minutes, 20 seconds
Episode Artwork

An fara musayar fursunoni mafi girma tsakanin Yemen da 'yan tawayen Houthi

Daga cikin labarun dashirin wannan lokaci ya tsakuro akwai taron da kasaashn Larabawa suka gudanar dominm kawo karshen matakin saniyar ware da suka mayar da Syria, sai kuma musayar fursunoni  da aka fara tsakanin gwamnatin Yemen da 'yan tawayen Houthi. A gabashin Afirka kuwa, hasarar rayuka aka samu a yayin da wasu mutane fiye da 10 suka tagayyara a Kenya saboda azumin mutuwa da ssuke yi a wani mataki na gaggawar saduwa da  Yesu Almasihu.
4/15/202318 minutes, 45 seconds
Episode Artwork

'Yan bindiga sun sace mutane 100 da suka hada da mata da kananan yara a Zamfara

Sama da mata da kananan yara 100'yan ta'adda suka yi garkuwa da su a dajin da ke gefen garin Wanzamai na jihar Zamfara da ke tarrayar Najeriya.Lamarin dai ya faru ne sakamakon kashe wasu 'yan ta'adda hudu da jami'an tsaron da ke baiwa garin kariya suka yi.A cikin shirin mu zagaya Duniya da kesaba waiwayar wasu daga cilkin muhiman al'amuran da suka auku tare da Nura Ado Suleiman daga nan Rfi.
4/8/202318 minutes, 32 seconds
Episode Artwork

Matsalar ta'addanci ta tilasta rufe makarantu a Burkina Faso.

Shirin 'Mu Zagaya Duniya'  ya saba waiwayar wasu daga cikin muhimman al’amuran da suka auku a makon da ya gabata ne. A wanna tasha ta Radio France Internationale yake zuwa muku. Daga cikin labarun da shirin wannan mako ya kunsa akwai rahoton da ya bayyana cewar matsalar hare-haren ‘yan ta’adda sun tilasta rufe akalla kashi 1 bisa 4 na yawan makarantu a Burkina Faso. A Najeriya kuma sabon gwmnan Zamfara mai  jiran  gado ya ce babu batun sulhu tsakanin gwamatinsa da ‘yan bindiga.  
3/25/202320 minutes
Episode Artwork

Boko Haram sun gwammaci mika kansu ga sojojin bayan kazamin fadan da suka gwabza da ISWAP

Mu Zagaya Duniya na wannan makon za a ji yadda daruruwan mayakan Boko Haram tare da Iyalansu suka gwammaci mika kansu ga sojojin Najeriya,biyo bayan kazamin fadan da suka gwabza da mayakan ISWAP a jihar Borno..Nura Ado Suleiman ne zai jagorancin shirin na wannan mako.
3/12/202320 minutes
Episode Artwork

Bitar mahimman al'amuran da suka faru a makon da ya gabata

Shirin 'Mu Zagaya Duniya' yana waiwaye ne a game da mahimman abubuwan da suka auku a makon daa ya gabata, kuma yana zuwa muku ne duk mako a wan a tashar. Shirin ya kawo mana labarin yadda a ranar 1 ga watan Maris ce hukumar zabe Najeriya ta ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023, da kuma yadda manyan kungiyoyin hamayya a kasar kamar su PDP da Labour suka yi watsi da sakamakon, suka kuma kai batun a gaban kotu.
3/4/202321 minutes, 52 seconds
Episode Artwork

Yan Najeriya da suka fusata sun fansama kan titunan wasu biranen kasar

A cikin shirin Mu zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, ya zakulo wasu daga cikin muhimman batutuwan da suka auku a makon da ya gabata.A wannan shiri za a ji yadda dubun dubatar yan Najeriya suka fansama kan tituna wasun wasu birane a sassan kasar domin zanga-zanga kan karancin sabbin takardun naira da kuma dakatar da amfani da tsaffin.
2/18/202320 minutes, 11 seconds
Episode Artwork

Girgizar kasa ta kashe mutane fiye da dubu 23 a Turkiya sa Syria

Daga cikin manyan al’amuran da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya waiwaya akwai halin da ake ciki a kasashen Turkiya da Syria, inda girgizar kasa ta kashe mutane fiye da dubu 23. Akwai kuma rahoto akan girgizar kasa mafi muni da aka gani a duniya cikin karni na 21.
2/11/202319 minutes, 48 seconds
Episode Artwork

Akalla kananan yara 49 suka mutu sakamakon nutsewa a ruwa a Pakistan

Shirin Mu zagaya Duniya na wannan mako ya mayar da hankali a kan Pakistan, in da akalla kananan yara 49 suka mutu sakamakon nutsewa a ruwa bayan kifewar Kwalekwalensu. Hatsarin ya auku ne a yayin da yawan wadanda suka mutu a harin bam din da aka kai kan Masallaci a Pakistan din ya kai mutane 100, yayin da wasu fiye da 200 suka jikkata.Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI zan jagoranci gabatar da shirin.
2/4/202318 minutes, 38 seconds
Episode Artwork

Burkina Faso ta nanata umarnin da ta baiwa sojojin Faransa na su fice daga kasar

‘Mu Zagaya Duniya’ mai bitar wasu daga cikin muhimman labaran, da suka fi daukar hankali a makon da ya kare, Nura Ado Suleiman daga sashin Hausa na RFI zan jagoranci gabatar da shirin. daga cikin labaren za ku ji cewa Gwamnatin sojin Burkina Faso ta nanata umarnin da ta baiwa sojojin Faransa cewa su fice daga kasar.
1/28/202320 minutes, 26 seconds